Fadakarwa game da da'awar canji a Najeriya.Daga:Limamin Central Mosque Birnin kebbi Imam Muhktar Abdullahi (Walin Gwandu)

Imam Muhktar Abdullahi

FADAKARWA GAME DA DA'AWAR CANJI A NAJERIYA DAGA: IMAM MUHKTAR ABDULLAHI (WALIN GWANDU


Hudubar Sallar Azumi 1st Shawwal 1437AH/6th July, 2016  a Masallacin Haliru Abdu Birnin Kebbi

Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, Wan nan da Ya sanya dare da yini masu maye wa juna, domin mai son ya tunatu ko ya yi godiya. Sai Ya fifita sashen ranaku a kan sashe da sashen watanni a kan sashe kuma shi ne Maigirma, Mai hikima.
Salati da sallama su tabbata ga manzon Allah wannan da ya buga mafi aiherin misalin tarbiyyar al-ummarsa, da alayensa da sahabbansa da wadanda suka jibince su har ya zuwa ranar hisabi.
Bayan haka kamar yadda muka sani muka gani cewa watan Ramalan mai albarka ya juya baya ya sake labulansa ya tafiyarsa. Allah Ya maimaita muna shi da aiheri da albarka. Kuma Allah Ya karba muna kyawawan ayukkan mu Ya gafarta sakaci da wuce wuri da kuskure da kasawa.
Jama'ar Musulmi, yana daga cikin abin da ya lazimce mu, a matsayin musulmin gaskiya riko da gaske da himmatuwa da darussan da muka samu a cikin watan Ramalan. Abin da ke tsarkake rai, ya gyara halaye, ya sanya nishadin zukata da hankali wajen aikata aiheri. Kuma saboda (darussan nan) su ne guzurin tsoron Allah wannan da yake aiheri ga duk wanda ya rike shi ya yi amfani da shi. Allah shi taimaka game da haka.
Har wa yau ba mu gushe ba a cikin lokutan da mutane ke neman canji a kasar nan kuma suna magana akai da yawa, sai dai ba wani abu na canjin a zuciyar mafi yawansu. Kai har ma mafi yawan su shirye suke su yaki dukan mai kokarin shiga tsakaninsu da zalunci da barna a cikin kasa.


Yaya kake neman canci ka raya cewa kana cikin masoyan sa masu taimaka wa gare shi aihali kai mal laifi ne daga cikin masu barna a cikin kasa? Yaya kake raya son gaskiya da adalci da amana, ka yi gurinsu aihaJi kai jagorane na karya ne da zalunci da Barna? Yaya canji ke gudana har ya kammala aihali mafi yawan mutane na taimaka masa ne da bakunansu, suna yakarsa da zukatansu da hannuwansu. Ya ya kasa za ta zabura ta habaka ta bunkasa aihali mutane masu kasala ne da son hutawa da zaman banza da jin dadi ga yawan koke da tuhumar juna da zace-zace da tarbon jita jita da yayata ta? Ya ya muke neman canji ba mu kusa da wadatar da kanmu da abinci da muke bukata, balle mu yi kokarin hana shigowa da kayan abincin da ke kwashe mafi yawan kudin shigar Nigeriya? Sai mu yaki shigowa da kayan abinci ta hanyar shagaltar da kanmu ga noma, har mu kai ga matakin wadatar da kanmu da abinci. Yawan shigowa da kayan abinci na gudana a gaban mu aihalin muna rayuwa a kasa maifadi, da yawan ruwan sama da ruwan kasa wadatacce, ga kasa mai kyau mai aibarka sai dai ba wadatar ma'aikata, ba isasshen ilimi, ba kayan aiki ingantattu na zamani domin cigaban noma, ba isasshen taliafi, ba saka hannun jari wadatacce. Amma mafiyan mu gafalallu ne ta yadda suke sha'awar cin abincin kasar waje da nuna gamsuwa da alfahari da jin kai. A lokacin da muke iya noma shi da kai gare shi a nan gida. Ga likitoci na bayyana cewa abincin da ke mahallinmu da magungunan mahallinmu su ne suka fi dacewa da jikinmu da lafiyarmu. Ya ban takaicin bin demuwa da rudani!!! Hakika wannan yanayi bai dace da kasar da ke noma tun tsohon zamani ba. Dole ne mu canza, mu samu cigaba a wannan bangaren mai muhimmanci.
Domin idan ba mu daina wannan mummunan sakacin ba, to duk ranar da aka rasa kudin shigar sayo abinci, yunwa na kama kasar nan a rasa mafita sai neman agaji da surutan banza.


Amma idan muka gyara, to kudin shigar da muka samu za su koma a wani bangare ko bangarorin gina kasa da cigabanta musamman a wannan lokaci na neman canji. Ga kuma nisantar da barazanar yunwa ga kasarmu. Allah shi taimake mu.
Amma taimakon da jihar Kabi ta bayar da na gwamnatin Nigeriya don karfafa noma da tallafa mai da kokarin da wasu manoma ke yi, to wannan wata farawa ce mai kyau da kokari abin yabo da godiya. Allah shi saka wa hukumar da aiheri. Tare da haka kamata ya yi mu dauki tallafin hukumar da kokarin da wasu manoma ke yi a matsayin farin farawa, domin mu kara kokari kwarai don cimma babbar manufa ta wadatar da kasar da abinci.

Bayan haka idan muka yi duba a fagen siyasa a lokacin da muke neman canji, tambayoyi na tasowa kamar haka:- Da wa da wa ne ke shiga siyasa domin kalmar Allah ta daukaka? Da wa da wa ke shiga siyasa don kariyar gaskiya da adalci da amana da aI'umma da kasa? Da wa da wa ne ke shiga siyasa domin talakawansa da kasarsa na a zuciyarsa?
Mafi yawa ba su gushe ba suna sha'awar su ci su sha su yalwata, su ji dad'i, su nutse a ciki, bisa jinin jama'a da dukiyar kasa, banda satar dukiyar jama'a kasa da ake yi ta hanya mai ban tsoro.
Muna maganar son gaskiya da adalci da amana da muhimmancinsu aihali muna rosa su da miyagun dabi'un mu. Muna kasala da jan jiki wajen gina al'umma da kasa hakikance. Muna koke muna zagi da tuhuma ba mu gabatar da abin da ake bukata ga gina aI'umma. Balle mu kara kokari da aiki mai kyau ga maslahar talakawa da kasa. Allah madaukaki ko ya yi gargadi daga karya da cin amana sai Ya ce:- Ya ku wadanda suka yi imani don mi kuke fadin abin da ba ku aikata wa?
Ya



girma kwarai ga zama abin ki wurin Allah, ku fadi abin da ba ku aikatawa. Sai ya yi zargi, ya tsoratar, ya kyace. Siyasa da kasa na gyaruwa ne kawai ta hanyar jibinta jagoranci ga wadanda ba su nufin daukaka da barna a cikin kasa, wadanda in Allah ya ba su iko a cikin kasa suna tsayar da Sallah, su ba da Zakka, su yi umurni da kyakyawa su yi hani daga mummuna. Wadannan su ke jawo zaman lafiya da kwanciyar hankali ga jama'a da kasa. Daga nan sai habaka da cigaba su samu.
Ba mu gushe muna bukatar tsaro ba, muna nemansa. Sai dai tsaro ba ya zowa kyauta dole a biya farashinsa tare da neman sa da imani da aiki da gaskiya da adalci da amana, in ba haka ba ya zai zo da karya da zalunci da barna da cin amana da son rai. A a bai taba samuwa da wannan har abada, Hakika Allah ba ya canja yanayin mutane sai sun canja abin da suke ciki. Kuma Allah Ya Ce:- "Hakika mu ba mu tozarta sakamakon wanda ya kyautata aiki" kuma Ya Ce:- "Hakika Allah ba Ya gyara aikin mabarnata".
Kasar nan tamu ba ta gushe ba tana fama da ta'addanci da sunan addini, wanda ya yanke cibiyarsa a arewa maso gabas da matsalar masu son a raba kasa da kirkiro Biafara da yan ta'addar siyasa da tattalin arziki a Niger Delta da matsalar wasu manyan yan siyasa da aka zaba masu sha'awar girman kai da kama karya masu neman mayar da talakawan kasa bayinsu.

Wadannan matsaloli idan ba a kara tashi tsaye aka tinkare su da wuri ba da ikhlasi da tawakkali ga Allah Madaukaki mai iko ba, to suna iya wargaza kasa ko alal'akalla ta doge ita ba ta rayu ba, ba ta mutu ba. Allah ya tsare mu.
Amma su wadannan yan siyasar masu kirkiro dokoki da ke cin mutuncin kansu da kasarsu da jama'arsu, to idan har da gaske suke kamata ya yi su nemi a jefa kuri'ar raba gardama game da  sha'anninsu. Sai talakawa su duba wannan bukatar ta su ta rasa hakken tuhumarsu, bincikensu, da hukunta su idan sun yi wa talakawa da kasa ba daidal ba, domin sun fi karfin doka. Idan talakawa suka ga hakan ya dace sai su yarda su rinka taka su yadda suka ga dama. Kuma a koyaushe suka shigo neman zabe su bayyana wa talakawa, su ne masu son kama karya da fin karfin doka domin talakawan su ji dadin zaben su bisa hujja bayyananna.
Kuma matakan da Gwamnatin tarayya ke kokarin dauka a kan zababbun 'yan siyasa majalisar dattijai masu wuce wuri, matakai ne masu kyau da suka dace da duk wanda bai yi halin dattako ba, kuma tasarrufin su na iya jefa jama'a da kasa cikin mummunan hali. Allah Shi taimaki masu kokarin daidaita lamurra, Shi saka masu da alheri.
A karshe duk mai son duniyarsa da lahirarsa su yi kyau sai ya tashi haikan ya yi aiki tukuru bisa kyakkyawar manufa da ilmi da gaskiya. Shi yasa muke ganin littafen Allah cike da maganar sai wadanda suka yi imani suka yi aikin kwarai duk sa'ar da ya ke maganar tsira ko samun nasara a rayuwa ko duka.
Kuma Allah Madaukaki na cewa:- Kuma ka ce ku yi aiki, Allah zai ga aikinku da Manzonsa da muminai, sannan a mayar da ku zuwa ga Masanin gaibi da abin da ya bayyana sai Ya ba ku labarin abin da kuka kasance kuna aikatawa.
Kamar yadda Manzon Allah ya karantar da cewa:- Mafi alherinku, shi ne mafi amfaninku ga mutane. Allah shi samu a cikinsu.

Imam Mukhtar Abdullahi
         (Walin Gwandu)











Post a Comment

RUBUTA SHARHI KO RA'AYINKA KAN WANNAN LABARI

Previous Post Next Post

Celebrity Gifts

Facebook

Latsa nan ka shiga group namu na WhatsApp domin samun labarai kai tsaye https://chat.whatsapp.com/EcJXY08Ikrx63mQ7F6TJfL

Domin zama wakilinmu garinku LATSA NAN

Korafi/ Shawara/ Tuntube mu LATSA NAN